Libiya Ta Fitar Da Sammacin Kame Wasu 'Yan Sudan Da Chadi
(last modified Sun, 06 Jan 2019 09:37:48 GMT )
Jan 06, 2019 09:37 UTC
  • Libiya Ta Fitar Da Sammacin Kame Wasu 'Yan Sudan Da Chadi

Kasar Libiya ta fitar sammaci 37 na kame wasu 'yan tawayen kasashen Chadi da kuma Sudan dama wasu 'yan Libiya, da ake zargi da hannu a hare haren da aka kai kan wasu cibiyoyin man fetur da kuma wani sansanin soji.

Sammacin dai ya shafi 'yan tawayen Chadi 22, da 'yan tara da kuma 'yan Libiya shida a cewar kamfanin dilancin labarai na France-Presse.

Dukansu dai an zarginsu da hannu a hare haren da aka kai a kan cibiyoyin man fetur a gabashin Libiya a shekara 2018 da kuma sansanin sojin sama na Tamenhant, dake gabashin Tripoli.

A cewar sanarwar data kunshi sammacin, 'yan Libiyan da ake zargi sun bukaci taimakon 'yan tawayen kasashen Sudan da kuam Chadi domin kai hare haren.