An Nada Sabon Firaminista A Kamaru
Shugaba Paul Biya na Jamhuriya Kamaru, ya nada, Joseph Dion Ngute, dan asalin yankin masu magana da turancin Ingilishi a kudu maso yammacin kasar a matsayin sabon firaministan kasar.
Kafin nada shi a matsayin firaminista, Mista Dion Ngute, na rike da mukamin minista a fadar shugaban kasa, kuma kafin hakan ya taba zama wakilin kasar ta Kamaru a kwamitin kare hakkin bil adama na Majalisar Dinkin Duniya.
A yanzu Ngute, zai maye gurbin Philemon Yang, wanda ke shugabancin gwamnatin kasar ta Kamaru yau kusan shekara tara.
Nadin Joseph Dion Ngute, mai shekaru 64, shi ne mataki na farko da shugaban kasar ta Kamaru, Paul Biya, ya dauka tun bayan sake zabensa a watan Oktoba na shekara data shude a wani wa'adin mulki.
sabon firaministan kasar Joseph Dion Ngute, ya fito ne daga yankin kudu maso yamma na masu magana da harshen tirancin Ingilishi mai fama da matsalar tsaro mai nasaba da masu fafatukar a ware na kasar ta Kamaru tun cikin shekara 2017.