Jami'an Tsaro A Kasar Kamaru Sun Kashe Wasu Yan Bindiga A Kasar
Majiyar jami'an tsaron kasar Kamaru daga garin Bamenda ta bayyana cewa jami'an tsaron kasar sun kashe wasu mutane dauke da makamai su 7 a wani sumamaye da suka kaiwa mabuyarsu.
Majiyar Muryar JMI ta nakalto ma'aikatar tsaron kasar tana bayyana haka a ranar Lahadin da ta gabata, ta kuma kara da cewa jami'an tsaron har'ila yau san sami nasara lalata wani sansanin horar da mayaka na kungiyar masu sun ballewa daga kasar a yankin da ake magana da harshen turanci.
Banda haka majiyar ta kammala da cewa sun sami makamai da kayakin aikin soje masu yawa a wurin. Tun cikin watan Octoban shekara ta 2017 aka soma tashe-tashen hankula a yankin masu magana da harshen ingilishi a arewa maso yammacin kasar kamaru. Kuma ya zuwa yanzu dubban mutane ne suka rasa rayukansu, daga cikinsu akwai jami'an tsaro da dama da aka kashe.
Masu magana da harshen turacin ingilishi a kasar Kamaru sune kashe 20 % na yawan mutanen kasar miliyon 20. Kuma suna ganin gwamnatin masu rinjaye wadanda suke magana da harshen faransanci ta waresu daga mukamai da kuma razikin kasar.