Sojojin Halifa Haftar Sun Fara Shirin Kwace Tripoli Babban Birnin Kasar Libya
(last modified Thu, 17 Jan 2019 11:53:07 GMT )
Jan 17, 2019 11:53 UTC
  • Sojojin Halifa Haftar Sun Fara Shirin Kwace Tripoli Babban Birnin Kasar Libya

Wasu majiyoyin Diblomasiyya sun bayyana cewa sojojin Halifa Haftar a kasar Libya sun fara shirin kwace iko da birnin Tripoly Babban birnin kasar wanda zai kawo karshen gwamnatin hadin kan kasa wacce Fa'iz Suraj yake jagoranta.

Jaridar -Al-Arabiyya Al-Jadidah ta nakalto wasu majiyoyin gwamnatocin kasashen Libya da Masar suna fadar haka. Labarin ya kara da cewa kafin haka halifa Haftar ya tattauna a asirce tare da shuwagabannin kabilun kasar ta Libya kafin ya fara wannan ynkurin. 

Wasu labaran sun nuna cewa gwamnatin kasar Hadaddiyar Daular larabawa UAE tana goyon bayan wannan yunkurin, a yayinda gwamnatin kasar Masar ta ki amincewa da hakan, take kuma ganin cewa yin hakan zai jawowa kasar takunkuman kasa da kasa. 

Har'la yau a cikin watan Decemban shekarar da ta gabata ce Janar Halifa Haftar mai ritaya ya gana da jami'an gwamnatin kasar Italia, da kuma jakadan Amurka a kasar Tunisia wanda kuma shi ne ke kula da al-amurna kasar Libya a gwamnatin shugaba Donal Trunp inda ya gana tare da su mai yuwa kan wannan matakin da yake son dauka.