MDD Ta Nuna Damuwarta Da Halin Da Kasar Libya Take Ciki
(last modified Sat, 19 Jan 2019 06:38:28 GMT )
Jan 19, 2019 06:38 UTC
  • MDD Ta Nuna Damuwarta Da Halin Da Kasar Libya Take Ciki

Jakadan MDD na musamman a kasar Libya ya bayyana cewa kasar Libya, musamman yankin kudancin kasar, har yanzun yana cikin mumunan hali na tabarbarewar harkokin tsaro.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto Gassan Salama jakadan MDD na musamman a kasar ta Libya yana fadar haka a jiya Jumma'a a lokacinda yake gabatar da rahoto dangane da kasar ta Libya ga komitin tsaro na majalisar.

Dangane da fadace-fadace a birnin Tripoli babban birnin kasar a baya-bayan nan, Gassan Salama ya ce, har yanzun ana ci gaba da yaki a tsakanin bangarori daban daban a birnin. Sannan ya zuwa yanzu an kashe akalla mutane 10 a yayinsa wasu 41 suka ji rauni. 

Kasar Libya ta fada cikin tashe-tashen hankula ne tun bayan boren mutanen kasar wanda ya kifar da gwamnatin Mu'ammar Kazzafi a shekara ta 2011.

Sannan a halin yanzu kasar tana da gwamantoci biyu, daya wacce Fa'iz Suraj yake jagoranta a birnin Tripoli, a yayinsa Janar Halifa Haftar yake jagorantar wata gwamnatin a birnin Bengazi daga gabacin kasar.