MDD: Dubban Mazauna Arewa Maso Gabashin Najeriya Suna Yin Hijira
(last modified Wed, 23 Jan 2019 17:47:14 GMT )
Jan 23, 2019 17:47 UTC
  • MDD: Dubban Mazauna Arewa Maso Gabashin Najeriya Suna Yin Hijira

Kakakin Majalisar Dinkin Duniya ne ya bayyana cewa; sabbin tashe-tashen hankulan da suke faruwa a cikin yankin arewa maso gabashin Najeriya sun sa dubban mazauna yankin yin gudun hijira

Farhan Haqq wanda ya gabatar da taron manema labaru ya ce; A bisa rahotannin da suke da su ta hanyar Majalisar Dinkin Duniya, daga watan Nuwamba na 2018 fada a tsakanin sojoji da masu dauke da makamai a yankin arewa maso gabashin kasar, musamman Jahar Borno ya sa mutane 80,000 yin hijira.

Kakakin Majalisar Dinkin Duniyar ya kara da cewa: Ya zuwa yanzu mutanen da suka zama 'yan gudun hijira a yankin arewa maso gabashin kasar sun kai miliyan daya da dubu dari takwas

Farhan Haqq ya kuma ce; Majalisar Dinkin Duniyar tana nuna damuwarta akan karuwar tashe-tashen hankula a yankin, haka nan kuma cikasa din da ayyukan agaji suke fuskanta a yankin

Kakakin Majalisar Dinkin Duniyar ya kuma bukanci ganin dukkanin bangarorin da suke fada da juna da su kare ruyukan fararen hula

Da akwai mutane fiye da miliyan bakwai da suke bukatuwa da tallafi a cikin yankin kamar yadda kungiyoyin agaji na Majalisar Dinkin Duniya su ka ambata