Kamaru : Amnesty Ta Bukaci A Sallami 'Yan Adawan Da Ake Tsare Da
(last modified Tue, 29 Jan 2019 16:13:41 GMT )
Jan 29, 2019 16:13 UTC
  • Kamaru : Amnesty Ta Bukaci A Sallami 'Yan Adawan Da Ake Tsare Da

Kungiyar kare hakkin bil adama ta kasa da kasa Amnesty International, ta yi kira ga hukumomin Jamhuriya Kamaru, dasu sallami dukkan 'yan adawan da ake tsare, ciki har da jagoran 'yan adawan kasar dake ci gaba da bayyana kansa a matsayin wanda ya lashe zaben shugabancin kasar.

A sanarwar data fitar, kungiyar ta Amnesty, ta bukaci hukumomin Kamarun su sallami 'yan adawan da kuma masu zanga zangar da aka cafke makon jiya, ba tare da wata wata ba.

Darectar kungiyar ta Amnesty reshen Afrika ta yamma da tsakiya, Samira Daoud, ta ce maimakon mahukuntan Kamarun su dauki matakai na kyautata al'amuran kare hakkin bil adama a kasar, sun fi gane su dinga shan suka, wanda kuma a cewarta dole a kawo karshen hakan.

Da yammacin jiya Litini ne aka cafke madugun 'yan adawa na kasar ta Kamaru, Maurice Kamto, wanda ya zo na biyu a zaben shugaban kasar ta Kamaru, da shugaba Paul Biya ya lashe. 

Matakin da gamayar kungiyoyin kare hakkin bil adama a tsakiyar Afrika jam'iyyarsa ta (Redhac), ta bayyana cewa ya sabawa dokar kasar da kuma dokokin kasa da kasa.

Ita kuwa babbar jam'iyyar adawa ta kasar (MRC), danganta tsare jagoran nata tayi da siyasa da kuma marar dalili, tare da kuma kira ga magoya bayanta da su kwantar da hankali.

A ranar Asabar ne jam'iyyar ta MRC, ta gudanar da zanga zanga a fadin kasar, ta kalubalantar sake zaben shugaban kasar Paul Biya wanda ya shefe shekaru 36 kan madafun iko.