Kamaru : 'Yan Adawan Da Ake Tsare Da Sun Fara Yajin Cin Abinci
(last modified Fri, 01 Feb 2019 04:48:04 GMT )
Feb 01, 2019 04:48 UTC
  • Kamaru : 'Yan Adawan Da Ake Tsare Da Sun Fara Yajin Cin Abinci

Madugun 'yan adawa a Jamhuriya Kamaru da kuma wasu makusantansa da ake tsare da, sun fara yajin cin abinci, a wani mataki na kalubalantar tsarewar da aka masu.

Maurice Kamto, shugaban jam'iyyar adawa ta MRC, wanda ya ayyana kansa a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar da ya gabata, da kuma wasu makusantansa da ake tsare da sun fara yajin cin abincin ne a jiya Alhamis, har sai lokacin da aka sallame su.

Ana dai zargin jagoran 'yan adawan ne da laifuka guda takwas, da suka hada da kiran tawaye, cin zarafin kasa, bore da tada hankali.

An dai cafke su ne a farkon makon nan, kuma a cewar wasu majiyoyi ana sa ran gabatar dasu gaban kotu yau Juma'a.

Duk da tsarewar da ake wa jagoranta da jiga jigai na jam'iyyar, MRC ta kira wara sabuwar zanga zangar lumana a gobe Asabar, kuma akwai yiwuwar wasu jam'iyyun adawa su shiga zanga zangar a cewar wani jigo a jam'iyyar.