An Kashe Sojojin Kasar Libya Hudu A Kudancin Kasar
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i35049-an_kashe_sojojin_kasar_libya_hudu_a_kudancin_kasar
Wata majiyar jami'an tsaro a kasar Libya ta bayyana cewa akalla sojojin kasar karkashin Halifa Haftar 4 ne suka rasa rayukansu a wani fafatawa da suke yi da wasu yan bindiga a kudancin kasar.
(last modified 2019-02-02T12:05:51+00:00 )
Feb 02, 2019 12:05 UTC
  • An Kashe Sojojin Kasar Libya Hudu A Kudancin Kasar

Wata majiyar jami'an tsaro a kasar Libya ta bayyana cewa akalla sojojin kasar karkashin Halifa Haftar 4 ne suka rasa rayukansu a wani fafatawa da suke yi da wasu yan bindiga a kudancin kasar.

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya nakalto Ahmad Almismari kakakin sojojin da ake kira "Sojojin kasar Libya" karkashin ikon Janar Khalifa Haftar mai ritaya yana cewa an kashe sojojin guda 4 ne a wani fafatawa da suka shiga da yan ta'adda na kasar Chadi a wani wuri kolomita 60 daga garin Sabhah daga kudancin kasar.

Almismari ya kara da cewa sojojin kasar ta Libya sun sami nasarar kubutar da garin Ghadwah inda aka yi ta fafatawar daga hannun yan ta'addan.

Kasar Libya dai fada cikin tashe-tashen hankula tun bayan faduwar gwamnatin Gaddafi a shekara ta 2011 a lokacinda yan tawaye masu samun goyon bayan kasashen yamma suka yi masa tawaye.