Nijar : Boko Haram Ta Kashe Mutum 6 A Tummur
(last modified Sat, 02 Feb 2019 16:57:10 GMT )
Feb 02, 2019 16:57 UTC
  • Nijar : Boko Haram Ta Kashe Mutum 6 A Tummur

Rahotanni daga Jamhuriya Nijar na nuni da cewa wani sabon hari da ake dangantawa dana kungiyar Boko Haram, ya yi ajalin mutum shida a wani kauye dake kudu maso gabashin kasar, a garin Tummur dake kusa da Tarayya Najeriya a yankin tafkin Chadi.

Majiyoyi daga yankin sun shaidawa kamfanin dilancin labaren AFP cewa, maharan sun kashe mutanen shida ne a cikin daren jiya Juma'a wajajen karfe goma na dare agogon wurin.

Bayanai sun nuna cewa ko a karshen watan Janairu da mukayi ban kwana dashi, mayakan na Boko haram sun kashe mutun hudu, a garin Bosso dake makobtaka da garin na Tummur.

Garuruwan na Bosso da kuma Tummur wadanda ke yankin tafkin Chadi, sun jima suna fuskantar hare hare na kungiyar ta Boko Haram.

Hare haren kuma na zuwa ne bayan wami mummunar farmaki da jami'an tsaron kasar ta Nijar suka kai kan sansanonin mayakan na Boko haran a yankin na tafkin Chadi inda suka kashe sama da 200 daga cikinsu a cewar rundinar sojin kasar.

Hukumomin Nijar dai sun damu da hare haren da kungiyar ta Boko haram ke kaiwa, musamman kan sansanonin soji, inda suke kwasar makamman yaki, lamarin da a cewar ministan tsaron kasar ta Nijar, Kalla Mountari, abun damuwa ne kasancewar zai iya karawa kungiyar karfi, musamman a wannan lokaci da kogin Komadugu ke kan kifewa, wanda dama shi ne ke hana mayakan tsallakawa zuwa cikin kasar.

Idan ana tune a wani taronsu a ranar 29 ga watan Nawamba bara, shuwagabannin kasashen yankin da suka hada da Chadi, Najeriya, Nijar, Kamaru sun nemi tallafin kasashen duniya don murkushe kungiyar ta Boko Haram.