Sojojin Halifa Haftar A Libya sun Kwace Garin Darne Gaba Daya.
Majiyar sojojin kasar Libya wadanda suke biyayya ga Janar Halifa Haftar mai ritaya ta bara labarin cewa sojojin kasar sun sami nasara mamaye garin Drne dake gabacin kasar gaba dayansa.
Tashar talabijin ta Skey News ta bayyana cewa sojojin kasar ta Libya sun kwace garin ne daga hannun yan ta'adda wadanda suke iko da garin tun da dadewa.
Kafin haka ma sojojin na kasar Libya sun kwace mafi yawan garin na Darneh , amma akwai wasu wurare a cikin garin inda yan ta'addan suka ja daga, wanda kuma aka dauki kwanaki 50 ana fafatawa da su kafin an kwace wadannan wurare.
Majiyar ta kara da cewa a daren jiya Asanar ne sojoji na kasar Libya suka yi kawanya wa wasu manya manyan gine-gine biyu wadanda yan ta'addan suke boye a cikinsu do su mika kai amma hakan bata samu ba.
Wannan ya sa suka yi amfani da karfi don kwace gine-ginen.