Gwamnatin Libiya Ta Bukaci Taimakon Kwamitin Sulhu Na MDD
Gwamnatin hadin kan kasa ta Libiya ta bukaci majalisar sulhu ta majalisar Dinkin Duniya da ta dauki matakin dakatar da dakarun tsaron kasar karkashin janar Khalifa Haftar ci gaba da hare-haren da suke kaiwa kudancin kasar
Tashar talabijin Aljazera ta nakalto Salah Al-Mujrabi wakilin kasar Libiya a Majalisar Dinkin Duniya na neman kwamitin sulhu na Majalisar da ya dauki matakan gaggauwa na dakatar da hare-haren da dakarun tsaron kasar karkashin jagorancin Janar Halifa Haftar suke kaiwa kudancin kasar.
A nata bangare tawagar wakilincin majalisar Dinkin Duniya dake kasar ta Libiya cikin wani bayyani da ta fitar ta ce akwai bukatar takaita hare-haren da sojojin Libiyan ke kaiwa a kudancin kasar da nufin yaki da ta'addanci.
A kwanakin baya-bayan nan dakarun khalifa haftar sun tsanaita kai hare-hare a yankunan kudancin kasar, inda a makon da ya gabata bayan ruwan wuta da suka yi a yankunan dake kusa da filin jirgi na matatar man Al-fil dake kudancin kasar, sun kuma hana tashin wani jirgi fajinsa a yankin.
Gwamnatin hadin kan al'ummar kasar ta Libiya dake samun goyon bayan kasashen Turai ta bayyana hakan a matsayin ta'addanci da kuma lafin take hakin bil-adama.
Tun a shekarar 2011 ne kasar Libiya ta fada cikin rikici bayan wani bore da matasan kasar suka yi na neman sauyi gwamnati, wanda hakan ya bawa kasar Amurka da kungiyar tsaron Nato damar amfani da karfi soji wajen hambarar da gwamnatin marigayi kanal Mu'amar Kaddafi tare kuma da yi masa kisan gilla.
A halin da ake ciki yanzu kasar ta Libiya nada gwamnatoci guda biyu, da suka hada da gwamnatin hadin kan kasar dake samun goyon bayan kungiyoyin kasa da kasa wacce hedkwatarta ke tripoli babban birnin kasar sai kuma Majalisar birnin Tabruk dake da mazauni a gabashin kasar wacce take samun goyon bayan rundunar tsaron kasar karkashin jagorancin janar Khalifa Haftar.