MDD Ta Jaddada Bukatar Kawo Karshen Rikicin Siyasar Libiya
(last modified Wed, 20 Feb 2019 10:21:48 GMT )
Feb 20, 2019 10:21 UTC
  • MDD Ta Jaddada Bukatar Kawo Karshen Rikicin Siyasar Libiya

Majalisar dinkin duniya ta jadadda bukatar ganin an kawo karshen rikicin siyasar da ya dabaibaye kasar Libiya.

Manzon musammam na MDD ne kan rikicin Libiya, Ghassan Salame, ya bayyana hakan, inda ya jaddada bukatar ganin an kawo karshen rikicin siyasar da kasar ke fama dashi, yau da shekaru takwas.

Mista Salame ya bayyana haka ne lokacin da yake ganawa da Agila Saleh, shugaban majalisar wakilan gwamnatin gabashin kasar ta Libiya.

Wata sanarwa da shirin wanzar da zaman lafiya na MDD a Libya ya fitar, ta ce Ghassan Salame ya jaddada kudurin MDD na aiki tare da al'ummar kasar game da hukumomi ta yadda za su zama na bai daya, da ingiza tattaunawa kan harkokin siyasa da ayyukan majalisun dokoki.

Duk da yarjejeniyar zaman lafiya da aka cimma karkashin MDD da kafa gwamnatin hadin kan kasar a 2015, har yanzu Libiya na fama da rarrabuwar kawuna saboda siyasa, tsakanin gwamnatocin yammaci da gabashin kasar.