Sojojin Libya Sun Kwace Garin Murzuk Daga Hannun Yan Ta'adda
Sojojin kasar Libya karkashin shugabancin Janar Halifa Haftar mai ritaya sun sami nasarar korar yan ta'adda daga garin Murzuk babban birnin lardin Murzuk dake kudu maso yammacin kasar.
Tashar talabijin ta Sky News ta bada labarin cewa sojojin kasar ta Libya karkashin jagorancin Khalifa Haftar sun sami nasarar kwace garin ne bayan fafatawa da yan ta'adda wadanda suke iko da garin tun da dadewa.
A cikin makon da ya gabata ma, sojojin na kasar ta Libya sun kwace iko da rijiyar man fetur mafi girma a yankin kudu maso yammacin kasar da ake kira rijiyar Ashararah daga hannun yan ta'adda.
Tun cikin watan da ya gabata ne sojojin kasar ta Libya suka fara ayyukan sojoji masu yawa a yankin kudancin kasar don kubutar da shi daga hannun yan ta'adda wadanda suke dade suna iko da shi.
Duk da cewa kasar Libya a halin yanzu tana da gwamnatoci biyu a kasar amma gwamnatin da ke karkashin ikon Halifa Haftar ce take rile da mafi yawan yankunan kasar da aka kwace daga hannun yan ta'adda.