Feb 21, 2019 12:21 UTC
  • Moroko: An Yi Taho Mu Gama A Tsakanin Jami'an Tsaro Da Malaman Makarantu Masu  Zanga-zanga

Kamfanin dillancin labarun Faransa ya ce; Da dama daga cikin malaman makarantun masu Zanga-zanga sun jikkata sanadiyyar raunukan da su ka samu daga amfani da karfi na jami'an tsaro

Malaman dai suna nuna kin amincewarsu ne da kokarin rusa makarantun gwamnati da kuma daukar malamai 'yan kwantiragi

Kungiyar Malaman makarantu ta kasar Moroko ta nuna cikakken goyon bayanta akan masu Zanga-zangar, sannan kuma ta bukaci su gudanar da yajin aiki

A cikin watannin bayan nan, malaman makarantu a kasar Moroko suna yawaita yin Zanga-zanga domin nuna kin amincewarsu da siyasar tattalin arzikin kasar wacce ta shafi rayuwarsu ta aiki

 

Tags