Aljeriya: An Yi Zanga-zangar nuna kin amincewa da tsayawa takarar shugaba Butefliqa
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i35249-aljeriya_an_yi_zanga_zangar_nuna_kin_amincewa_da_tsayawa_takarar_shugaba_butefliqa
Kungiyoyi daban-daban na kasar Aljeriya sun gudanar da wata Zanga-zanga ta nuna kin amincewa da tsayawa takarar shugabancin Abdulazizi Butafkilqa wanda yake fama da tsufa da rashin lafiya
(last modified 2019-02-17T03:08:17+00:00 )
Feb 17, 2019 03:08 UTC
  • Aljeriya: An Yi Zanga-zangar nuna kin amincewa da tsayawa takarar shugaba Butefliqa

Kungiyoyi daban-daban na kasar Aljeriya sun gudanar da wata Zanga-zanga ta nuna kin amincewa da tsayawa takarar shugabancin Abdulazizi Butafkilqa wanda yake fama da tsufa da rashin lafiya

Masu Zanga-zangar sun kirayi shuagaba Abdulazizi Butefliqa da ya sauya ra'ayinsa, ya janye daga tunanin sake tsayawa takarar shugabancin kasar a zabe mai zuwa

Jam'iyyar da take mulki a kasar ta Aljeriya ta sake tsayar da shugaba Abdulaziz Butefliqa a matsayin dan takarar shugaban kasar a zabe mai zuwa.

Butefliqa dan shekaru 82 ya zam shugaban kasar Aljeriya ne tun a 1999 ya kuma yi zango hudu na shugabancin kasar a jere.

Za a yi zaben shugaban kasar ta Aljeriya ne a ranar 18 ga watan Aprilu na 2019