Mar 07, 2019 09:52 UTC
  • Najeriya: 'Yan Sanda Sun kame Mutane Fiye Da 300 Kan Zabukan Da Suka Gabata

Rundunar 'yan sandan Najeriya ta ce ta kame mutane fiye da 300 bisa zarginsu da aikata ba daidai ba a lokacin gudanar da zabukan shugaban kasa da na 'yan majalisun dattijai da wakilai a wancan makon da ya gabata.

Kamfanin dillancin labaran AFP ya bayar da rahoton cewa, babban sufeton 'yan sanda na Najeriya Muhammad abubakar Adamu ya bayyana cewa, a halin yanzu akwai mutane 323 da aka kama kuma ake tsare da su, bisa aikata laifuka daban-daban a lokacin zabukaan da suka gabata.

Ya kara da cewa, 'yan sanda ba su yi kasa a gwiwa ba wajen dauklar dukkanin matakan da suka dace domin tunkarar zabukan ranar Asabar mai zuwa, kuma ba za su daga wa kowa kafa ba matukar ya taka doka da kuma saba ka'ida.

Kungiyoyin farar hula a Najeriya sun ce akalla mutane 53 ne suka rasa rayukansu a tashe-tashen hankulan da suka faru a yayin gudanar da zabukan shugaban kasa da 'yan majalisar tarayya a fadin kasar, daga ciki kuwa har da 'yan sanda biyu.

Tags