Sudan: Albashir Ya Yi Wa Wasu Manyan Jami'an Soji Ritaya
Mar 10, 2019 15:45 UTC
Shugaban kasar Sudan Umar Hassan Albashir ya yi wa wasu daga cikin manyan jami'an sojin kasar ritaya.
Kamfanin dillancin labaran Anatoli ya bayar da rahoton cewa, a wani mataki da shugaban kasar Sudan Umar Hassan Albashir ya dauka na yin garambawul a cikin rundunar sojin kasar, ya yi wa wasu daga cikin manyan jami'an sojin kasar ritaya, haka nan kuma ya kara wa wasu mukamai.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da kasar ke fuskantar gagarumar zanga-zanga domin yin kira Albashir da ya sauka daga kan karagar mulki, wadda ya kwashe shekaru 30 a kanta.
Tuna cikin watan Disamban 2018 da ta gabata ce aka fara gudanar da zanga-zangar ta Sudan, domin kokwa kan matsalolin tsadar rayuwa, daga bisani kuma ta rikide ta koma ta adawa da gwamnati.