Al'ummar Garin Syrte Sun Shiga Mawuyacin Hali Sakamakon Killacewar Kungiyar ISIS
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i370-al'ummar_garin_syrte_sun_shiga_mawuyacin_hali_sakamakon_killacewar_kungiyar_isis
Majalisar Mashawartan garin Syrte na kasar Libiya ta Sanar da cewa Al'ummar garin na cikin mawuyacin hali tun bayan da mayakan ISIS suka yi kaka gida a cikin garin.
(last modified 2018-08-22T06:57:46+00:00 )
Feb 06, 2016 07:42 UTC
  • Al'ummar Garin Syrte Sun Shiga Mawuyacin Hali Sakamakon Killacewar Kungiyar ISIS

Majalisar Mashawartan garin Syrte na kasar Libiya ta Sanar da cewa Al'ummar garin na cikin mawuyacin hali tun bayan da mayakan ISIS suka yi kaka gida a cikin garin.

A wata sanarwa da ya fitar yau Assabar,Shugaban Majalisar Mashawarta na garin Syrte dake arewacin kasar Libiya ya ce Al'ummar garin na cikin mawuyacin hali tun bayan da mayakan ISIS suka yi kaka gida a cikin garin, inda suke bayar da wasu Umarni da ya yi hanun rika da koyarwar Addinin Islama.

Kungiyar Ta ISIS ta Tilastawa shugabanin Makarantun garin da su dinga koyawa dalibansu munanan Akidar ta'addanci domin su yi amfani da Taliban wajen ci gaba da kai hare-haren ta'addanci a kasar ta Libiya

Har ila yau shugaban Mashawartan ya ce mayakan na ISIS sun mayar da massalatai gurin koyar da aiyukan soja na mayakan kungiyar.

Yanzu haka dai kungiyar Ta ISIS na rike da gariruwan Syrte da Bn Jawad a kasar ta Libiya inda suke kokarin mayar da cibiyoyin man fetur din kasar a matsayin guraren da za su dinga samar musu da gudaden shiga.