Damuwar kasashen dake amfani da kudin CFA kan yanyin tattalin arzikin yankin
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i3718-damuwar_kasashen_dake_amfani_da_kudin_cfa_kan_yanyin_tattalin_arzikin_yankin
Kasashen dake amfani da kudin CFA sun nuna damuwarsu kan matsalarda tattalin arzikin kasashen ya ke fuskanta
(last modified 2018-08-22T06:58:07+00:00 )
Apr 10, 2016 11:10 UTC
  • Damuwar kasashen dake amfani da kudin CFA kan yanyin tattalin arzikin yankin

Kasashen dake amfani da kudin CFA sun nuna damuwarsu kan matsalarda tattalin arzikin kasashen ya ke fuskanta

A jiya Assabar ministocin kasashe 15 masu amfani da kudin CFA sun gudanar da wani taro a birnin Yawunde na kasar Kamaru domin gudanar da bincike kan matsalar da tattalin arzikin kasashen ke fuskanta sakamakon faduwar farashin albarkatun kasar da suke sayarwa a kasuwanin Duniya.wannan taro ya samu halartar Ministan kudin kasar Faransa Michel Sapain.

A jawabin buda taron Piraministan kasar Kamaru Philemon Yang ya bayyana cewa kasashen dake amfani da kudin CFA na fuskantar matsalar kudi da tattalin arziki biyo bayan rashin daidaiton kudun na CFA da kuma matsalar kasuwanci na cikin gida.wasu daga cikin mahalarta taron sun bukaci da a daina amfani da kudin CFA tare da samar da kudin bai daya na kasashen Afirka.

bayan kasar Camores daga cikin kasashen dake amfani da kudin CFA a kwai kasashen takwas dake yammacin Afirka da suka hada da Benin, Burkina Faso, Cote D'ivoire, Guine Bisaou, Mali, Niger, Senegal da Togo, sai kuma kasashe 6 dake tsakiyar Afirka da suka hada da Kamaru, Afrika ta tsakiya, D/Congo, Gabon, Guine equatoral, da kuma Tchadi.