Jakadun Kasashen Faransa, Birtaniya Da Spain Na Ziyara A Libya
Apr 14, 2016 06:06 UTC
Yau Alhamis jakadun kasashen Faransa, Spain da kuma Birtaniya sun isa kasar Libya, domin nuna goyan bayan kasashen su ga sabuwar gwamnatin hadaka ta kasar dake samun goyan bayan MDD, karkashin jagorancin Fayez al-Sarraj.
Wannan dai ita ce ziyara farko ta jam'ian diflomatsiya kasashen Turai a Tripoli tun bayan da kungiyar EU ta rufe ofisoshin jakadancin ta a Tripoli babban birnin kasar a shekara 2014 sakamakon yakin da kasar ke fama da shi.
Wannan ziyara kuma na zuwa ne kwana guda bayan wace shugaban diflomatsiyan Italiya ya kai a kasar domin nuna goyan bayan kasar sa ga sabuwar gwamnatin hadaka ta Libya.
Tags