Shugaban Kasar Tunusiya Ya Bayyana Goyon Bayansa Ga Kungiyar Hizbullah
Shugaban kasar Tunusiya Beji Caid Al-Sebsi ya bayyana cewar kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon kungiya ce ta gwagwarmaya da take fada da haramtacciyar kasar Isra'ila, don haka ba kungiya ce ta ta'addanci ba.
Shugaban kasar Tunusiyan ya bayyana hakan ne a wata hira da yayi da tashar talabijin ta BBC sashin larabci inda ya ce kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ba kungiyar ta'addanci ba ce, wata kungiya ce ta gwagwarmaya wacce ta ke fada da wuce gona da irin haramtacciyar kasar Isra'ila.
Shugaba Al-Sebsi ya kara da cewa kungiyar Hizbullah dai wani bangare ne na gwamnatin kasar Lababon, don haka gwamnatin kasar Tunusiya ba za ta dau wata matsaya wadda za ta kasance tsoma baki ne cikin harkokin cikin gidan wata kasa ba.
Shugaban na Tunusiya yana mayar da martani ne dangane da yadda wasu kungiyoyin kasashen larabawa bisa matsin lambar kasar Saudiyya suka bayyana kungiyar ta Hizbullah a matsayin kungiyar ta'addanci wanda tun a lokacin kasar Tunusiyan da wasu kasashen larabawan suka bijirewa wa wannan matsaya ta Saudiyya da kuma kin amincewa da hakan suna masu cewa kungiyar Hizbullah din wata kungiya ce ta gwagwarmaya da wuce gona da irin yahudawan sahyoniya.