Kira Domin Kafa Gwamnatin Hadin Kasa A Kasar Libya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i403-kira_domin_kafa_gwamnatin_hadin_kasa_a_kasar_libya
yin kira ga dukkanin bangarorin siyasar Libya da su amince da kafa gwamnatin hadin kan kasa.
(last modified 2018-08-22T06:57:46+00:00 )
Feb 07, 2016 02:16 UTC
  • Kira Domin Kafa Gwamnatin Hadin Kasa A Kasar Libya

yin kira ga dukkanin bangarorin siyasar Libya da su amince da kafa gwamnatin hadin kan kasa.

Kamfanin Dillancin Labarun Faransa ya nakalto Cobler yana yin kira ga dukkanin bangarorin siyasar Libya da su amince da kafa gwamnatin hadin kan kasa.

Martin kobler wanda shi ne manzon musamman na majalisar dinkin duniya a kasar ta Libya, ya gana da shugaban majalisar kasar Libya da duniya ta amince da ita, Aqilah Salih, a jiya asabar a garin Shahat, tare da yin kira a gare shi da majalisar da ya ke wakilta da su amince su kada wa gwamnatin hadin kan kasar kuri'a.

cobler ya kara da cewa; A halin da ake ciki batu mafi muhimmanci shi ne samar da ci gaba cikin hanzari a fagen siyasar kasar, ta hanyar amincewar majalisa da sunayen wadanda za su wakilici gwamnatin hadin kan kasa.

Tun a cikin watan Decemba na shekarar da ta gabata ne dai bangarorin da su ke da sabani da juna a kasar ta Libya suka rattaba hannu akan kafa gwamnatin hadin kan kasa, sai dai har yanzu sun kasa cimma matsaya wajen kafa ta.