Mayakan Boko Haram Sun Kashe Sojojin Kamaru Ukku
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i4153-mayakan_boko_haram_sun_kashe_sojojin_kamaru_ukku
Wasu majiyoyin labarai sun bayyana cewa mayakan boko haram sun kashe sojojin
(last modified 2018-08-22T06:58:09+00:00 )
Apr 20, 2016 13:15 UTC
  • Mayakan Boko Haram Sun Kashe Sojojin Kamaru Ukku

Wasu majiyoyin labarai sun bayyana cewa mayakan boko haram sun kashe sojojin

Wasu majiyoyin labarai sun bayyana cewa mayakan boko haram sun kashe sojojin Kamaru 3 sun kuma raunata wasu ukku a wani harin ba zata da suka kai masu a arewacin kasar.

Kamfanin dillancin laraban APF ya bayyana cewa harin ya auku ne a yankin Dabanga dake kan iyakar kasar ta tarayyar Nigeria.

Mayakan boko haram dai sun kashe mutane fiye da dubu 15 a arewacin Nigeria tun shekara 2009. inda a shekara ta 2015 kungiyar ta kwace iko da wasu yankuna da dama a arewa maso gabacin kasar. Kasashen Nigeria Niger Camaroo da Chadi ne suka fi fama da mayakan na boko haram a yankin.