Gwamnatin Libiya Ta Kori 'Yan Gudun Hijira Afirkawa Sama Da 200
Rahotanni daga kasar Libiya sun bayyana cewar gwamnatin kasar ta kori sama da 'yan gudun hijira 200 da suka fito daga kasashen Afirka daban-daban daga kasar inda suka koma da su zuwa kasashensu.
Kafar watsa labaran Africanews ta jiyo kakakin kwamitin sanya ido kan bakin haure na kasar Libiyan Hosni Jumaa Ayyad yana fadin cewa mun kori bakin haure kimanin 204 da suka fito daga kasashe daban-daban da suka hada da Mali, Nijar, Gambiya, Eritrea da Ivory Coast. Jami'in ya kara da cewa an tura keyan wadannan mutanen ne zuwa kasashensu bayan an tattauna da ofisoshin jakadancinsu da ke birnin Tripoli, babban birnin kasar Libiyan.
Korar wadannan bakin hauren dai ta zo ne a daidai lokacin da Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD take nuna damuwarta kan yiyuwar nutsewar sama da bakin haure 500 a Tekun Mediterraniya a makon da ya wuce.
Mafi yawa daga cikin bakin hauren dai sun iso kasar Libiyan ne a kokarinsu na haurawa zuwa kasashen Turai.