An cabke 'yan boko haram a sansanin 'yan gudun hijra
Ma'aikatar tsaron kasar Kamaru ta sanar da kame wasu mayakan boko haram a sansanin 'yan gudun hijrar Najeria dake cikin kasar
Kafar watsa labaran Afirka time ta nakalto Ma'aikatar tsaron kasar Kamaru na cewa Jami'an tsaro sun kame wasu mayakan boko haram 4 a sansanin 'yan gudun hijrar Najeria na garin Miawao dake arewacin kasar
Ma'aikatar tsaron ba tare bayyana mayakan boko haram din da ta kame ko 'yan wata kasa ne ba, ta tabbatar da cewa su nada hannu kan hare-haren ta'addanci baya bayan nan da ake kaiwa garin Maroua, sun fake a sansanin 'yan gudun hijrar ne a yayin da Dakarun tsaron suka kai farmaki baya-bayan nan a sansanin boko haram din dake arewacin kasar, wannan lamari dai ya sanya magaban kasar ta Kamaru karfafa matakan tsaro a sansanin 'yan gudun hijrar.
A 'yan kwanakin da suka gabata, Dakarun tsaron kamaru sun sanar da dasa wasu tagawan bama-bamai a garin Maroua, bayan bayyanan sirrin da suka samu daga wajen jama'a sun tabbatar da cewa wadanda suka dasa Bom din sun koma sansanin 'yan gudun hijra na garin Minawao, lamarin da ya sanya suka gudanar da bincike tare da cabke wadannan 'yan ta'adda guda 4.