Fada Tsakanin Sojojin Libya Da Masu Dauke Da Makamai
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i4489-fada_tsakanin_sojojin_libya_da_masu_dauke_da_makamai
Fada Tsakanin Sojojin Libya Da Masu Dauke Da Makamai.
(last modified 2018-08-22T06:58:11+00:00 )
Apr 28, 2016 08:00 UTC
  • Fada Tsakanin Sojojin Libya Da Masu Dauke Da Makamai

Fada Tsakanin Sojojin Libya Da Masu Dauke Da Makamai.

An yi fada a tsakanin sojojin kasar Libya da kuma wasu masu dauke da makamai a yankin Banighazi.

Rahotannin da su ke fitowa daga yankin Banighazi da ke gabacin kasar Libya sun ce; Tun a makon da ya shude ne dai ake batga-kashi a tsakanin dakarun da su ke a karkashin Janar Halifa Haftar da kuma mayakan da su ke dauke dauke da makamai a yankin, da su ka hada da Ansarus'shari'a masu alaka da alqaeda.

A wani rahoton da tashar telbijin din almayadeen ta nakalto ta ce; sojojin Libya sun kuma ja daga domin kwato da garin Misratah daga hannun 'yan ta'adda.

A cikin makwannin bayan nan dai sojojin gwamnatin kasar ta Libya suna samun nasara akan kungiyoyin 'yan ta'adda.