Yan Ta'addan Da'ish Suna Barazana Ga Cibiyoyin Man Fetur Na Kasar Libiya
Wakilin Majalisar Dinkin Duniya na musamman a kasar Libiya ya bayyana cewa: Hare-haren ta'addancin kungiyar Da'ish suna barazana ga cibiyoyin man fetur na kasar Libiya.
Wakilin Majalisar Dinkin Duniya na musamman a kasar Libiya Martin Kobler ya bayyana tsananin damuwarsa kan hare-haren baya-bayan nan da mayakan kungiyar ta'addanci ta Da'ish suka kai kan cibiyar man fetur a Libiya, yana mai fayyace cewa irin wannan hare-hare babbar barazana ce ga tattalin arzikin kasar.
Wannan furuci na Martin Kobler ya zo ne a daidai lokacin da 'yan kungiyar ta'addanci ta Da'ish suka kai wasu jerin hare-haren wuce gona gona da iri kan cibiyar man fetur da ke yankin Arkub a yammacin garin Ajdabiya a arewacin kasar Libiya. Harin na 'yan kungiyar ta'addanci ta Da'ish yayi sanadiyyar mutuwar wasu daga cikin masu gadin cibiyar.
Rikicin siyasar da Libiya da afka ciki tare da bullar ayyukan ta'addanci a kasar sun taimaka wajen rage yawan man fetur da kasar ta Libiya ke hakowa a tsawon 'yan shekarun baya-baya nan, inda tun daga shekara ta 2011 kasar ta koma tana hako man fetur kashi daya cikin biyar na yawan man da ke hakowa a baya.
Masana harkar tattalin arziki suna bayyana cewa; Tattalin arzikin Libiya ya dogara ne a kan man fetur da take fitarwa, inda kayayyakin bukatun al'ummar kasar kashi 90 cikin dari gwamnati tana sayowa ne daga irin ribar da take samu daga man fetur kamar sauran kasashen Larabawa musamman saudiyya.
Har ila yau masu fashin baki suna bayyana cewa: Daya daga cikin manyan dalilan da suka ingiza kasashen yammacin Turai da Amurka shiga cikin tawagar 'yan tawayen Libiya domin kifar da gwamnatin marigayi Mu'ammar Gaddafi a shekara ta 2011 akwai kwadayin son mamaye tarin arzikin man fetur da kasar ta mallaka. Kamar yadda kungiyar ta'addanci ta Da'ish ita ma ta fantsama cikin kasar ta Libiya domin samun kudaden shiga da nufin bunkasa ayyukanta na ta'addanci a duniya daga tarin arzikin man Libiya.
A halin yanzu da kungiyar ta'addanci ta Da'ish ta ga al'ummar Libiya suna kokarin dinke barakar da ke tsakaninsu ta hanyar kafa gwamnatin hadin kan kasa domin tunkarar tarin matsalolin da suke addabar kasar musamman barazanar ayyukan ta'addanci, don haka kungiyar ta Da'ish ta tsiri kai hare-hare kan cibiyoyin man fetur na kasar da nufin tarwatsa su kowa ma ya rasa.