Sama da Mutane 30 aka kashe A Libiya watan da ya gabata.
Majalisar Dinkin Duniya ta Sanar da kashe Mutane sama da 30 watan da ya gabata a kasar Libiya
A wata Sanarwa da ta fitar Jiya Lahadi, Dakarun tsaron da Sulhu na MDD dake kasar Libiya wata UNSMIL, Sanadiyar tashin hankali dake faruwa a kasar Mutane 33 ne suka rasa rayukansu yayin da wasu da dama suka jikkata A watan Avrilun da ya gabata.
Rahoton ya ce daga cikin wadanda suka rasa rayukan nasu 14 fararen hula ne daga cikin a kwai kananen Yara biyu da Mata guda 4. A cewar UNSMIL, asarar rayukan da aka samu sanadiyar fashewar ababen fashewa ne a bangare guda.
Kungiyoyin 'yan ta'adda da dama sun yi amfani da rikicin kasar ta Libiya domin samun gindin zama a kasar daga cikin irin wadannan kungiyoyi har shahararar kungiyar Ta'addasncin nan ta ISIS.
Saidai duk da irin tafiyar hawainiyar da kafuwar Gwamnatin hadin kai kasar ke yi, Al'umma nada kyakkyawan fata dangane da sabuwar Gwamnatin.