Shugaban Kasar Kamaru Paoul Biya Zai Fara Ziyarar Aiki A Nigeria
Shugaban kasar Kamaru Paul Biya zai fara ziyarar aiki na kwanaki biyu a tarayyar Nigeria daga yau Talata.
Shugaban kasar Kamaru Paul Biya zai fara ziyarar aiki na kwanaki biyu a tarayyar Nigeria daga yau Talata. Jaridar Daily Trusta ta Nigeria ta nakalto Kakakin fadar shugaban kasa a Abuja, Femi Adesina yana fadar haka a jiya da yamma. Femi ya kara da cewa shugaba Biya zai taho tare da Matarsa da kuma wasu manya manyan jami'an gwamnatinsa. Har'ila yau za'a yi masa tarba ta musamman a fadar shugaban kasa a yau da Rana.
Adesina ya ce ana saran bangarorin biyu zasu tattauna batutuwan da suka shafi tsaro, wadanda suka hada da yaki da ta'addanci, aikata laifuffuka na kan iyakoki da kuma wasu da dama.
Kafin shugaba biya ya kammala ziyararsa na kwanaki biyu ana saran kasashen biyu zasu sanya hannu kan yerjejeniyoyi da dama.