An Kashe Wani Babban Jami'in Tsaron Libiya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i472-an_kashe_wani_babban_jami'in_tsaron_libiya
A ci gaba da gumurzu tsakanin 'yan bindiga da Jami'an tsaron, wani babban jami'in tsaron kasar ya rasa ransa a yau.
(last modified 2018-08-22T06:57:47+00:00 )
Feb 08, 2016 07:10 UTC
  • An Kashe Wani Babban Jami'in Tsaron Libiya

A ci gaba da gumurzu tsakanin 'yan bindiga da Jami'an tsaron, wani babban jami'in tsaron kasar ya rasa ransa a yau.

Kafar watsa labaran Alyaumu sabi;i ta kasar Masar ta nakallto wata jami'ar Asibitin garin Bangazi na cewa, A ci gaba da gumurzu tsakanin 'yan bindiga da jami'an tsaron kasar wani babban jami'in tsaron kasar ya rasa ransa a yau, yayin da wasu uku na daban suka jikkata.

Fadiya Alragasi ta kara da cewa a jiya lahadi ma rikici ya yi sanadiyar mutuwar mutane biyu tare da jikkata wasu uku na daban.

Rikicin na kasar Libiya na ci gaba duk da cewa an kafa Gwamnatin hadin kai 'yan kasa kalkashin jagorancin Fa'iz Assiraj.