Kungiyar ISIS ta mayaye yankuna biyu a arewacin Libiya
May 06, 2016 05:17 UTC
Kungiyar 'Yan ta'addar ISIS sun mamaye yankuna biyu a kusa da garin Misrata dake arewacin kasar Libiya
A daren Jiya Alkhamis, mayakan kungiyar ISIS sun kai hari kan yankunan Alkadahiya da wadi-zamzam dake kusa da garin Misrata na arewacin Kasar Libiya tare da mamaye su.
Wannan farmaki na zuwa ne a yayin da Dakarun tsaron Libiya ke shirye-shirye kai farmaki garin Syrte wanda shine sansanin 'yan ta'addar na ISIS a kasar.
Rahotanni sun ce 'yan ta'addar ISIS da dama ne dake garin Bangazi zuwa tsare zuwa garin na Syrte.
A cikin kwanakin da suka gabata, kungiyar 'yan ta'addar ta ISIS ta hana dukkanin fararen hula ficewa daga garin na Syrte.
Tags