'Yan Bokoharam Sun Kashe Fararen Hula A Kamaru
'Yan Kungiyar Bokoharam Sun Kai Wani Sabon Hari tare da kashe mutane da dama.
Cibiyar watsa labarun nan ta Afirca Taimes ta ambato wani jami'in sojan kamaru, Janar Bouba Debekreo yana cewa; A wani harin da kungiyar ta bokoharam ta kai a garin Taher da ke kuma da iyaka da Najeriya, sun kashe fararen hula uku.
Janar Dobekreo ya kara da cewa; Sojojin Kamaru tare da rundunar hadin guiwa sun bi sawuna 'yan ta'addar tare kuma da kora su.
Harin dai ya zo ne bayan ziyarar kwanaki biyu da shugaban kasar Kamaru ya kai zuwa Najeriya inda ya tatauna hanyoyin dakile hare-haren kungiyar ta bokoharam.
A cikin watannin bayan nan dai an sami koma baya na hare-haren da kungiyar ta bokoharam ta ke kai wa a cikin Najeriya da kuma kasashen da su ke makwabtaka da ita.