Komawar Dakarun tsaro mabiya Kaddafi a Kasar Libiya
Dakarun tsaron dake goyon bayan tsohon shugaban Libiya Mu'amar Kaddafi sun fara komawa kasar Su domin taimakawa a tsarkake kasar daga 'yan ta'adda ISIS.
Rahotanni daga Kasar Libiya na cewa tuni dai Dakarun tsaron kasar na hanun damar tsohon Shugaban kasar marigayyi Mu'amar Kaddafi da suka fice daga cikin kasar bayan kashe shi a yayin juyin juya hali na shekarar 2011 sun fara komawa kasar Su, kuma tuni suka hade da bataliyar Sjin yammacin kasar domin taimakawa a tsarkake garin Syrte wacce ma'aifar tsohon shugaban kasar Kaddafi ne.
Rahoton ya ce manufar komawar wadannan Sojoji dai shi ne mayar da martabarsu domin samun matsayi bayan tsarkake kasar daga 'yan ta'adda.
A halin da ake ciki, garin na Syrte na kalkashin 'yan ta'addar ISIS, yayin da Dakarun hadin gwiwa na kasar da kasashen Birtaniya, Faransa, Italiya, Jamus da Amurka ke shirye-shiryen kai musu hari.
Tun bayan rashin nasarar da ta fuskanta a kasashen Siriya da Iraki, kungiyar ta ISIS ta fara tarewa a kasar Libiya.