Kasashen Larabawa Sun bukanci A Dage Takunkumin Sayarwa Libya Da Makamai
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i4939-kasashen_larabawa_sun_bukanci_a_dage_takunkumin_sayarwa_libya_da_makamai
Shugaban gwamnatin hadin kan kasar Libya ya bukaci kungiyar kasashen
(last modified 2018-08-22T06:58:14+00:00 )
May 08, 2016 12:23 UTC
  • Kasashen Larabawa Sun bukanci A Dage Takunkumin Sayarwa Libya Da Makamai

Shugaban gwamnatin hadin kan kasar Libya ya bukaci kungiyar kasashen

Shugaban gwamnatin hadin kan kasar Libya ya bukaci kungiyar kasashen larabawa su taimaka a dagewa kasarsa takunkumin sayan makamai da aka dora mata sannan a saki kudaden kasar wadanda aka hana tabawa a kasashen duniya.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto daga jaridar الیوم السابع ta kasar masar tana fadar haka a yau Lahadi. Ta kuma kara da cewa Fa'iz Siraj shugaban gwamnatin hadin kan kasar Libya ya fadi haka ne a lokacinda yake jawabi a cibiyar kasashen larabawa da ke birnin Alkahiri. shugaba Siraj ya kara da cewa gwamnatinsa tana yaki da kungitar Daesh ta yan ta'adda kuma yan ta'adda basu san iyaka ba, don haka suna iya fadawa ko wace kasa daga cikin kasashen duniya.

A nashi bangaren babban sakataren kungiyar kasashen Larabawa Nabil Al-Arabi ya tabbatarwa shugaban gwamnatin hadin kan kasar Libya cewa, kasashen Larabawa zasu ci gabata da goyon bayan gwamnatin hadin kai a kasar ta Libya, sannan zasu tabbatar da cewa sun taimaka mata kan abubuwan da zasu dawo da zaman lafiya a kasar.