An Gano Kaburburan Gama Gari A Kasar Libya
Majiyar sojojin kasar Libya ta bayyana cewa ta gano kaburburan gama gari har 30
Majiyar sojojin kasar Libya ta bayyana cewa ta gano kaburburan gama gari har 30 a wasu yankuna daga gabacin kasar. Jaridar al-yaumussabeh ta kasar Masar ta nakalto Salim Gafir kakakin wata rundunar sojojin kasar yana bayyana haka a yau Litinin a birnin Bengazi. Mai maganan ya kara da cewa tare da taimakon kungiyar bada agaji ta Hilal Ahmar an fara aikin tono kaburburan. Majiyar ta kara da cewa akwai zaton kungiyar ta'adda ta Daesh ce ta kashe mutanen ta bisne su a wata gona a yankin Al-faakaat kusa da birnin Bengazi.
Har'ila yau yau labaran ya kara da cewa sojojin kasar ta libya a halin yanzu sun yi wa garin sirt wanda yake hannun yan ta'adda kawanya a kokarin da suke da kwace shi daga hannunsu.