Yan Ta'adda Sun Kakkabo Jirgin Yakin Gwamnatin Libiya A Gabashin Kasar
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i502-yan_ta'adda_sun_kakkabo_jirgin_yakin_gwamnatin_libiya_a_gabashin_kasar
Rundunar sojin gwamnatin Libiya ta sanar da cewa; Jirgin yakinta guda da kai farmaki kan sansanin 'yan ta'addan kungiyar Da'ish a yankin gabashin kasar a jiya Litinin, 'yan ta'adda sun kakkabo jirgi.
(last modified 2018-08-22T06:57:47+00:00 )
Feb 09, 2016 01:58 UTC
  • Yan Ta'adda Sun Kakkabo Jirgin Yakin Gwamnatin Libiya A Gabashin Kasar

Rundunar sojin gwamnatin Libiya ta sanar da cewa; Jirgin yakinta guda da kai farmaki kan sansanin 'yan ta'addan kungiyar Da'ish a yankin gabashin kasar a jiya Litinin, 'yan ta'adda sun kakkabo jirgi.

Kakakin rundunar sojin gwamnatin Libiya da kasashen duniya suka amince da halaccinta da ke da sansani a garin Baidha a gabashin kasar Nasir Al-Ha'si ya bayyana cewa; Jirgin saman yakin gwamnatin kasar ya kai hari kan sansanin kungiyar ta'addanci ta Da'ish a yankin Wa'di-Khalid da ke nisan kilomita 1100 da gabashin birnin Tripoli fadar mulkin kasar, amma 'yan ta'addan sun samu sa'ar kakkabo jirgin, sai dai matukin jirgin mai suna Yunus Addilani ya samu nasarar fice daga cikin jirgin tare da tsira daga shiga hannun 'yan ta'addan.

A bayan sanar da faduwar jirgin wasu rahotonni sun habarta ce matsalar inji ne ta janyo faduwar jirgin, amma daga baya aka samu tabbacin cewa kakkabo jirgin aka yi da makami mai linzami.