Kotun Kasar Libiya Ta Sake Dage Shari'ar Da Ake Yi Sa'adi Gaddafi
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i5035-kotun_kasar_libiya_ta_sake_dage_shari'ar_da_ake_yi_sa'adi_gaddafi
Rahotanni daga kasar Libiya sun bayyana cewar wata kotu a birnin Tripoli, babban birnin kasar Libiya ta dage shari'ar da take yi wa dan tsohon shugaban kasar Libiyan Mu'ammar Gaddafi, wato Sa'adi Gaddafi har sai karshen watan Mayun nan.
(last modified 2018-08-22T06:58:15+00:00 )
May 11, 2016 01:01 UTC
  • Kotun Kasar Libiya Ta Sake Dage Shari'ar Da Ake Yi Sa'adi Gaddafi

Rahotanni daga kasar Libiya sun bayyana cewar wata kotu a birnin Tripoli, babban birnin kasar Libiya ta dage shari'ar da take yi wa dan tsohon shugaban kasar Libiyan Mu'ammar Gaddafi, wato Sa'adi Gaddafi har sai karshen watan Mayun nan.

Kamfanin dillancin labaran Faransa ya bayyana cewar a jiya Talata ne aka sake gurfanar da Sa'adi Gaddafi a gaban kotun da ke birnin Tripoli bisa zargin hannu cikin irin zubar da jinin 'yan adawa masu kokarin kifar da gwamnatin mahaifinsa a shekara ta 2011 inda bayan wani lokaci alkalin kotun ya dage shari'ar har zuwa ranar 25 ga watan Mayun nan da muke ciki don ci gaba da shari'ar.

Masu shigar da kara dai suna zargin Sa'adi Gaddafi dan shekaru 43 a duniya ne da laifin sace mutane, keta hurumi, azabtarwa, amfani da mukaminsa ta yadda bai dace ba bugu da kari kan ba da goyon bayan na kudi da makamai wajen zubar da jinin masu boren da yayi sanadiyyar kifar da gwamnatin Mu'ammar Gaddafin a shekara ta 2011.

Bayan kifar da gwamnatin Gaddafin, Sa'adi Gaddafi ya gudu zuwa kasar Nijar inda daga baya gwamnatin kasar ta mika shi ga gwamnatin kasar Libiyan don yi masa shari'a.