Gwamnatin Libiya Ta Kafa Dakarun Tsaron Fadar Shugaban Kasa
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i5044-gwamnatin_libiya_ta_kafa_dakarun_tsaron_fadar_shugaban_kasa
Fira ministan gwamnatin hadin kan kasa a Libiya ya kafa dakarun tsaron fadar shugaban kasa da nufin kula da cibiyoyi da gine-ginen gwamnatin kasar.
(last modified 2018-08-22T06:58:15+00:00 )
May 11, 2016 04:52 UTC
  • Gwamnatin Libiya Ta Kafa Dakarun Tsaron Fadar Shugaban Kasa

Fira ministan gwamnatin hadin kan kasa a Libiya ya kafa dakarun tsaron fadar shugaban kasa da nufin kula da cibiyoyi da gine-ginen gwamnatin kasar.

Fira ministan gwamnatin hadin kan kasar Libiya Fayyaz al-Sarraj a jiya Talata ya sanar da kafa dakaru na musamman da ake kira da dakarun tsaron fadar shugaban kasa da zasu dauki alhakin kula da tsaron cibiyoyi da ma'aikatun gwamnati a birnin Tripoli fadar mulkin kasar.

Dakarun tsaron fadar shugaban kasar suna karkashin umurnin babban kwamandan rundunar sojin kasar ta Libiya ne amma suna da kasafin kudinsu na musamman da gwamnati zata dinga ware musu.