Samarda Rundunar Kare Fadar Shugaban Kasa A Libya.
Priministan kasar Libya ya bada sanarwar kafa rundunar kare fadar shugaban
Priministan kasar Libya ya bada sanarwar kafa rundunar kare fadar shugaban kasa a kasar. Tashar Lelevision ta labarai mai suna -Al-hadas-ta nakalto Fa'iz Siraja yana fadar haka a ranar talatan da ta gabata ya kuma kara da cewa rundunar kare fadar shugaban kasa tana da nauyin tabbatar da tsaro a dukkan gune gine da cibiyoyin gwamnatin a duk fadin kasar.
Bisa bayanan da Priministan ya yi , ya nuna cewa rundunar zata yi aiki karkashin babban hafsan hafsoshin sojojin kasar, amma a bisa a binda ya shafi bada umurni da kuma kudaden aiki rundunar tana zaman cin gashin kanta.
A dayan bangaren kuma Faiz Siraj ya bukaci majalisar dokokin kasar ta gudanar da zama don tattaunawa da kuma amincewa da gwamnatin hadin kan kasa da yake jagoranta. Wannan aikinta ne na asali kuma amincewa da gwamnatin hadin kan kasar da yake jagoranta zai taimaka wajen tafiyar da kasar cikin sauki.
A ranar 17 ga watan Satumban shekara ta 2015 ne, a wani taron tattaunawa ta yan siyasar kasar Libya wanda aka gudanar a birnin Assukhairat na kasar Morocco, suka amince da Fa'iz Suraj a matsayin shugaban gwamnatin hadin kan kasa da na kasar ta Libya, sannan a ranar a ranar 9 ga watan Decemba ya yi rantsuwar kama aiki a matsayin shugaban gwamnatin hadin kan kasar. Sai kuma a ranar 19 ga watan Jenerun shekara ta 2016 Fai'z Suraj ya bayyana sunayen majalisar ministocinsa.
Duk da cewa gwamnatin Priminista Suraja tana matukar kokarin kyawtata halin da kasar take ciki, amma rashin amincewa da gwamnatinsa wanda har yanzun majalisar dokokin kasar bata yi ba ya nuna cewa har yanzun akwai bangarorin biyu wadanda suke jin cewa ko wanne daga cikinsu yana cin gashin kansa.
Gwamnatin hadin kan kasar dai tuni ta kafa rundunar sojojin kasar don yakar kungiyar yan ta'adda ta Daesh wacce take iko da birnin Sirt mai arzikin man fetur . Ya kuma nada General Bashir Mohammad Al-qadi a matsayin komandan da zai jagoranci rundunar ta kwato yankunan kasar daga hannun kungiyar Daesh. Banda hada Suraj ya gargadi dukkan kungiyoyin da suke dauke da makami a kasar da kada su shiga cikin yaki da kungiyar ta Daesh ba tare da amincewar babban komandan sojojin kasar ba. A ranar Litinin da ta gabata ce majiyar sojojin kasar ta Libya ta bada sanarwan cewa rundunar sojojin kasar sun fara jan daga a kusa da cibiyan Daesh da ke garin «الجفره» dake kudancin birnin Sirt.
Kasashen Afrika da Larabawa sun bayyana damuwarsu da ikon da kungiyar Daesh ta shimfida a kasar Libya da kuma dangantakarta da kungiyoyin yan ta'adda wadanda suka hada da Boko Haran da kuma kungiyar Al-qaeda reshem Magrib.
Gwamnatin Suraja ta yi al-kawarin kyautata tattalin narzikin kasar ta Libya, saida a cikin yan shekarun da suka gabata mafi yawan rijiyoyi da cibiyoyin ajiye man sun lalace sadaniyar yakin da ake yi a cikin gida.
Kakakin ma'aikatar haka da sarrafa man fetura a kasar ta Libya ya bayyana a ranar Litinin da ta gabata a kan cewa, idan kellacewar da akewa tashar jiragen ruwa ta مرسی الحریقه ta ci gaba to kuwa samar da man fetur a rijiyoyin da suke kudancin kasar zasu tsaya a cikin makonni hudu masu zuwa .
Daga karshe shugaban kamfanin man fetur da kasar Mustafa San'ullah ya yi kira ga wadanda suke hana daukar danyen man fetur daga wasu tashojin jiragen ruwa daga kudancin kasar da su sake duba wannan matsayin da suka dauka, don hakan ba zai dore ba.