Yan Ta'addan Kungiyar Da'ish Sun Datse Kawunan Mabiya Addinin Kirista A Libiya
May 12, 2016 05:15 UTC
Yan kungiyar ta'addanci ta Da'ish masu kafirta musulmi sun aiwatar da hukuncin kisan gilla kan mabiya addinin kirista 'yan kasar Habasha da dama a gabar taken Libiya ta hanyar datse musu kawuna da kuma harbi da bindiga.
A wani sabon fyaifayi na bidiyo da kungiyar ta'addanci ta Da'ish mai kafirta musulmi ta watsa yana dauke da yadda 'yan ta'addan kungiyar Da'ish suka aiwatar da kisan gilla kan mutane 16 mabiya addinin kirista 'yan kasar Habasha a gabar tekun kasar Libiya.
Fyaifayin bidiyon na tsawon mituna 29 yana dauke da yadda 'yan kungiyar ta Da'ish suka datse kawunan kiristocin tamkar dabbobi, saura kuma aka kashe su ta hanyar harbi da bindiga.
Tags