Gumurzu Tsakanin Sojojin Libiya Da Gungun 'Yan Ta'adda A Wasu Yankunan Kasar
May 14, 2016 06:13 UTC
Dauki ba dadi tsakanin sojojin gwamnatin Libiya da wasu gungun 'yan ta'adda a yankunan gabashi da kuma arewacin kasar ya lashe rayukan mutane kimanin 30.
Rundunar sojin Libiya ta sanar da cewa: A dauki ba dadin da aka yi tsakanin sojojin gwamnatin Libiya da wasu gungun 'yan ta'adda a yankunan Qawa'rishah da Sabir da suke garin Benghazi a shiyar arewa maso gabashin kasar da suka kai ga lashe rayukan sojojin kasar akalla uku tare da na 'yan ta'adda da dama.
A gefe guda kuma sojojin gwamnatin Libiya sun samu nasarar halaka 'yan ta'addan kungiyar Da'ish 27 a wani dauki ba dadin da bangarorin biyu suka yi a yankin Sada'dah a kudancin garin Misratah a arewacin kasar ta Libiya.
Tags