Libya Da Tunisia Sun Maido Da Huldar Kasuwanci A Iyakarsu
May 15, 2016 06:30 UTC
Kasashen Libiya da Tunisia sun cimma matsaya guda akan sake tafiyar da harkokin kasuwanci a iyakar kasashen biyu.
kasashen biyu dai sun dakatar da harkokin kasuwanci tsakanin su a karshen watan Afrilu, kuma a cewar hukumomin yankin za'a maido da harkokin kasuwanci a wannan Litinin a yankin Ras Jedir.
bangarorin biyu sun cimma wannan matsaya a ce a ranar juma'a data gabata bayan shafe tsawan lokaci na tattaunawa, aman ko wanne bangare wajibi ne ya biya kudadan kwastom.
kasar Tunisia dai ta jima tana rufe wannan iyaka tsakanin ta da Libya saboda barazanar ta'adanci.
Tags