Martanin dakarun Yemen kan hare-haren Saudiya
Dakarun tsaron Yemen sun halba makamai masu Lizzami zuwa yankunan dake kan iyakokin kasar da Saudiya
Tashar telbijin din Almayaddin ta kasar Lobnon ta habarta cewa Sojoji da dakarun sa kai na kasar Yemen sun halba makamai masu Lizzami zuwa ga filin sauka da tashi na jiragen saman garin Jizan da barikokin sojin saudiya dake yankunan Asir da Najran a matsayin mayar da martani kan ci gaba da ta'addancin da masarautar Ali sa'oud ke yi a kasar.
Har ila Dakarun tsaron kasar sun kai wani farmaki a barikin sojin saudiya dake garin Asir, inda suka hallaka sojojin saudiya da dama tare kuma da mamaye barikin sojin.
A bangare guda Jiragen Yakin masarautar Ali sa'oud sna ci gaba da kai hare haren wuce gona da iri a yankuna daban-daban na cikin kasar ta yemen daga ciki har da babban birnin Sana'a, inda suka hallaka fararen hula da dama.