Gaargadi Akan Bunkasar Da'esh A Kasar Libya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i535-gaargadi_akan_bunkasar_da'esh_a_kasar_libya
Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadi akan yadda kungiyar Da'esh ( Isil) ta ke kokarin yaduwa a cikin kasar Libya.
(last modified 2018-08-22T06:57:47+00:00 )
Feb 09, 2016 15:32 UTC
  • Gaargadi Akan Bunkasar Da'esh A Kasar Libya

Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadi akan yadda kungiyar Da'esh ( Isil) ta ke kokarin yaduwa a cikin kasar Libya.

Jaridar Yaus-Sabi'i, ta Kasar Masar, ta ambato manzon musamman na majalisar dinkin duniya a kasar Libya, Martin Kobler yana yin gargadi da cewa; Da akwai hatsarin yaduwar ayyukan kungiyar 'yan ta'adda ta Da'esh a cikin yankunan Afirka da kuma Bokoharam a cikin Najeriya da Nijar da Chadi.

Bugu da kari, Kobler ya yi wani gargadin akan fadadar ayyukan ta'addanci na kungiyar Da'esh din a cikin kasar Libya, saboda haka ya bukaci da a yi gaggawar kafa gwamnatin hadin kan kasa a libyan.

Manzon na Majalisar Dinkin Duniyar a Libya ya kuma yi ishara da yadda ake nuna halin ko in kula akan hali da yanayin da kasar ta Libya ta ke ciki, sannan ya kara da cewa; "Al'ummar kasar sun sa ido suga an kafa gwamnatin hadin kan kasa domin suna da kyakkyawan fata akanta."

Tun a cikin watan Dcemba ne dai bangarorin da su ke da sabani da juna a kasar ta Libya su ka cimma yarjejeniyar kafa gwamnatin hadin kan kasa, sai dai har yanzu ba a kai ga kafa ta ba.