Libya : An Kashe Sojojin Gwamnatin hadaka 32
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i5377-libya_an_kashe_sojojin_gwamnatin_hadaka_32
A Libiya adadin sojojin gwamnatin hadaka na kasar da suka mutu a wani harin da aka kai da mota da kuma fafatawa da 'yan ta'adan IS ya kai 32.
(last modified 2018-08-22T06:58:17+00:00 )
May 19, 2016 06:41 UTC
  • Libya : An Kashe Sojojin Gwamnatin hadaka 32

A Libiya adadin sojojin gwamnatin hadaka na kasar da suka mutu a wani harin da aka kai da mota da kuma fafatawa da 'yan ta'adan IS ya kai 32.

Wata sanarwa da rundinar sojin ta wallaffa a shafin na twetter ta kuma ce an samu wasu sojoji 50 da suka raunana.

lamarin dai ya auku ne jiya Laraba a yankin Abou Grin dake da nisan kilomita 130 a yammacin Syrte.

tun da farko dai rundinar sojin kasar ta ce sojoji 18 ne suka rasu.