'Yan Kunar Bakin Wake Sun Kashe Mutane 6 A Kasar Kamaru
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i571-'yan_kunar_bakin_wake_sun_kashe_mutane_6_a_kasar_kamaru
Akalla mutane 6 sun rasa rayukansu yayin da wasu sama da 30 kuma suka sami raunuka sakamakon tagwayen hare haren kunar bakin wake da wasu 'yan ta'adda suka kai arewacin kasar Kamaru a yau Laraba.
(last modified 2018-08-22T06:57:47+00:00 )
Feb 10, 2016 12:03 UTC
  • 'Yan Kunar Bakin Wake Sun Kashe Mutane 6 A Kasar Kamaru

Akalla mutane 6 sun rasa rayukansu yayin da wasu sama da 30 kuma suka sami raunuka sakamakon tagwayen hare haren kunar bakin wake da wasu 'yan ta'adda suka kai arewacin kasar Kamaru a yau Laraba.

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya jiyo wasu ya jiyo wasu jami'an yankin suna fadin cewa lamarin ya faru ne a lokacin a lokacin da 'yan kunar bakin wake suka tayar da bama-baman da suke jikinsu a wajen wata jana'izar da ake yi a kauyen Nguetchewe da ke kimanin kilomita 10 daga kan iyakar kasar Kamarun da Nijeriya.

Wasu majiyoyin sun bayyana cewar daga cikin daga cikin wadanda wannan harin ya ritsa da su har da mata da kananan yara, kamar yadda wasu majiyoyin ma suka ce adadin wadanda suka sami raunukan ya kai mutane 50.

Ana nuna yatsar zargi wannan harin dai ga kungiyar nan ta Boko Haram wacce ta jima tana kai irin wadannan hare-hare na ta'addanci yankunan arewacin kasar ta Kamaru.