An dage Shari'ar da ake yi wa Sa'adi Ghaddafi
Kotu ta dage shara'ar da ake yiwa Dan tsohon shugaban Kasar Libiya Sa'adi Kaddafi
Tashar telbijin din Sky News ta habarta cewa a jiya Alkhamis kotun birnin Tripoli ta dage shara'ar da take yiwa Sa'adi Kaffafi da kuma Abdul..Mansur Shugaban Ma'aikatar Leken asiri na Gwamnatin Mu'amar Kaddafi zuwar ranar 12 ga watan yuni.
Kotun ta ce ta dauki wannan matakin ne bisa bukatar lauyoyin da ke kare wadanda ake zarkin.
A cewar magabatan kotun, ana zarkin Sa'adi Kaddafi da Laifin satar Mutane, cin zarafin Al'umma, keta hurumin 'yan kasar,amfani da kudin kasa wajen goyon bayan kungiyoyin dake dauke da makamai wajen kawar da wadanda suka yi juyin juya hali na watan Favrayu.
shi kuma Abdul..Mansur ana zarkin sa ne da laifin goyon bayan tsohon shugaban kasar Mu'amar kaddafi da kuma yin azaba ga matasan da suka yi juyin juya hali a kasar.