An Tabbatar Da Bullar Murar Tsuntsaye A Kamaru
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i5851-an_tabbatar_da_bullar_murar_tsuntsaye_a_kamaru
Hukumomin kasar ne suka tabbatar da bullar cutar mura tsuntsaye, bayan wani bincike da kwararu suka aiwatar a wata gona kiwan kaji dake kasar.
(last modified 2018-08-22T06:58:20+00:00 )
May 27, 2016 11:34 UTC

Hukumomin kasar ne suka tabbatar da bullar cutar mura tsuntsaye, bayan wani bincike da kwararu suka aiwatar a wata gona kiwan kaji dake kasar.

Alkalumen wucin gadi da hukumomin kasar suka fitar sun nuna cewa sama da kaji 15,000 ne suka mutu sanadanin mura, kuma tuni gwamnatin kasar ta sanar da daukan kwararen matakai na dakile yaduwar cutar.

Ministocin sadawa dana lafiya da kuma na kamun kifi ne suka sanar da hakan a yayin wani taron manema labarai a Yaoude babban birnin kasar.

Daga cen din kuma ga rahoto da wakilin mu Wada Alh. Ya hada muna.