Wa'adin Kafa Gwamnatin Hadin Kan Kasar Libya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i589-wa'adin_kafa_gwamnatin_hadin_kan_kasar_libya
An Tsaida Ranar 14 Ga Watan Febarairu Domin Kafa Gwamnatin Hadin Kan Kasar Libya
(last modified 2018-08-22T06:57:47+00:00 )
Feb 11, 2016 02:01 UTC
  • Wa'adin Kafa Gwamnatin Hadin Kan Kasar Libya

An Tsaida Ranar 14 Ga Watan Febarairu Domin Kafa Gwamnatin Hadin Kan Kasar Libya

Majalisar Kasar Libya ta tsaiwata wa'adain kafa gwamnatin hadin kan kasa daga nan zuwa 14 ga watan Febrairu, domin fitar da kasar daga matsalar tsaro.

A jiya laraba ne dai kamfanin dillancin labarun Faransa daga birnin Tripoli ya nakalto cewa; 'Yan majalisar kasar da su ke a gabacin kasar, sun amince da cewa daga nan zuwa ranar lahadin mako mai zuwa, za a kafa gwamnatin hadin kan kasa.

A jiya laraba ne dai, kwamitin majalisar mai mutane 9 ya kamata ya gabatar da sabbin sunaye na wadanda za su rike mukaman ministoci a sabuwar gwamnatin hadin kasar da za a kafa, sai dai shugaban kwamitin Fa'iz al-Siraj ya bukaci da a daga lokacin zauwa mako mai zuwa.

Mjalisar wacce duniya ta amince da ita, ta bukaci da a samar da sauye-sauye a cikin sunayen ministoci 32 da aka gabatar mata.

Tun a shekarar da ta gabata ne dai gwamnatoci biyu da ake da su a cikin kasar ta Libya su ka amince da kafa gwamnatin hadin kan kasa, sai dai har yanzu ba ta kai ga kafuwa ba.